Jump to content

Wq/ha/Floella Benjamin

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Floella Benjamin

Dame Floella Karen Yunies, Benjamin, Baroness Benjamin, OM, DBE, DL (an haife shi 23,ga watan Satumba, shekara ta 1949) yar wasan kwaikwayo ce ta Trinidadian-Birtaniya, mawaƙa, mai gabatarwa, marubuci kuma ɗan siyasa. An san ta a matsayin mai gabatar da shirye-shiryen yara kamar Play School,Play Away, Jamboree da Fast Forward. A ranar 28 ga watan Yuni, shekara ta 2010, an gabatar da Lady Benjamin zuwa House of Lords a matsayin abokiyar rayuwa wanda 'yan jam'iyyar Liberal Democrat suka zaba,

Zantuka

[edit | edit source]

"Floella Benjamin: 'Ni Miss Optimist. Ba na barin mummunan abubuwa su cinye ni'" (shekarar 2022) "Floella Benjamin: 'Ni Miss Optimist. Ba na barin munanan abubuwa su cinye ni'", The Guardian (12 ga watan Yuni, shekara ta 2022).

Ba abin da ya same ni. Mai kyau ko mara kyau. Domin ban taba waiwaya ba. Idan ka waiwaya baya, za ka kasance cikin matsala, za ka sha wahala daga bakin ciki, tabin hankali – a’a! Koyaushe duba. Bana barin munanan abubuwa su cinye ni, a'a. Domin ni ba wanda aka zalunta ba. Shi ya sa mutane ke ce mani, "Idan na ga murmushinki na kan ji dadi sosai, idan na ga jikinki, auranki, sai na ji kamar zan iya jurewa." Domin ni Miss Optimist! Lokacin da kake baƙar fata kana ɗaukar launinka tare da kai duk inda za kaje. Ina nan don ciyar da al'umma gaba kuma duk da cewa na sami cikas zan shawo kansu saboda ina aiki mai kyau. Na yi nasara Kuma ina gaya wa mata cewa za su iya yin nasara.